ABNA24 : Shugaban ya kara da cewa tuni makiya su na sauya gaskiya dangane da ayyukan da gwamnatin kasar Iran takewa mutanen kasar don cimma wannan manufar. Rouhani ya bayyana haka ne a safiyar yau Talata, a lokacinda yake shugabantar taron majalisar tattalin arzikin kasar a nan birnin Tehran.
Shugaban ya ce Jagoran juyin juya halin musulunci Ayatullahi sayyeed Aliyul Khamina’ii ya bayyana shirye-shiryen makiya na durkusar da tattalin arzikin kasar Iran, na karami da dogon ango, a cikin jawabnsa na baya-bayan nan, daga cikin har da yakin farfaganda don hana tattalin arzikin kasar ci gaba. Sannan da boye gaskiyar abinda yake faruwa a kasar. Daga karshe shugaban ya ce wadannan shirye-shirye biyu suna tafiya tare.
342/